Bankin Duniya zai taimakawa makwabtan Syria

Bankin Duniya na kokarin hada wani tsari da zai bayar da dauki ga 'yan gudun hijirar Syria a kasashen da ke makwabtaka da kasar.

Jami'an Bankin sun ce kasashen Lebanon da Jordan na daukar nauyi fiye da kima, hakan kuma ya sa suka soma tattaunawa da kasashen Larabawa masu arziki, game da yadda za a taimaka.

Bankin ya ce shirinsa ya samu karbuwa sosai, kuma yana fatan samun zubin farko cikin watanni hudu zuwa shidda masu zuwa.

Wannan shiri ya tanadi yarjejeniya da kasashen suka shiga da Bankin Duniya, inda zai ba su bashin kudin, su kuma su kai dauki ga 'yan gudun hijirar da ke kasashensu.

Miliyoyin 'yan gudun hijira ne suke tserewa zuwa kasashen da ke makwabtaka da Syria, mafi yawancinsu kuma su na kasar Turkiyya, amma kasashen da matsalar ta fi yi wa ciwo su ne Lebanon da Jordan.

'Taimaka wa Duniya'

A Lebanon yawan 'yan gudun hijirar ya kai kaso 20 cikin 100 na mutanen garin, kazalika kuma a Jordan sun kai kaso 20 cikin 100.

Kudin da gwamnati ke kashewa na zuwa ne daga kashi 85 cikin 100 na 'yan gudun hijirar da ke zama cikin gidaje ba a sansanonin 'yan gudun hijira ba, inda Majalisar Dinkin Duniya ke daukar nauyin su.

Gwamnati na biyan kudin asibiti da na makarantar 'yan gudun hijirar da basa cikin sansanoni, suna kuma samun wutar lantarki da ruwa, duk da cewar ana tallafa masu da kudaden da suke biya, dalilin haka ya sa zaman 'yan gudun hijirar ta ke kara wa gwamnatin kasar kudin da take kashewa.

Image caption Majalisar Dinkin Duniya ce ke daukar nauyin dawainiyar 'yan gudun hijirar Syria da ke sansanoni.

Ana wa Lebanon da Jordan kallon kasashen da basu da karfin tattalin arziki, shi ya sa Bankin Duniyar zai tallafa masu ta hanyar basu kananan basussuka.

Ana kyautata zaton za a samu karin taimako daga kasashe mafi karfin tattalin arziki a duniya su bakwai watau G7.