Guinea: Alpha Conde ya lashe zabe

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban kasar Guinea, Alpha Conde

Hukumar zaben kasar Guinea ta ce shugaba mai-ci, Alpha Conde ya samu nasarar sake dare wa karagar mulkin kasar karo na biyu.

Hukumar ta ce shugaba Alpha Conden ya samu kashi 58 cikin 100 na kuri'un da aka kada, yayin zaben shugabancin kasar ranar Lahadin da ta gabata.

Wannan sakamako dai yana nufin cewa ba a bukatar zuwa zagaye na biyu na zaben.

Sai dai kuma dan takarar babbar jam'iyyar adawa a kasar, Cellou Diallo ya yi watsi da sakamakon sannan kuma ya yi kira ga magoya bayansa da su fito zanga-zangar lumana.

Tun dai lokacin da aka fara kidayar kuri'a ranar Larabar da ta gabata ne Cellou Diallo ya sanar da fice wa daga jerin 'yan takara bisa zargin tafka magudi a lokacin zaben.

Sai dai kuma masu sanya ido daga Tarayyar Turai sun bayyana zaben da sahihi.