Amurka ta bai wa Kamaru motocin yaki

Hakkin mallakar hoto Screen Grab
Image caption Kamaru na fama da hare-haren kungiyar Boko Haram kamar makwabciyarta Najeriya

Shugaban dakarun Amurka na Afrika Janar David Rodriguez ya bai wa jamhuriyar Kamaru motocin yaki domin tallafa mata wajen yaki da kungiyar Boko Haram.

Babban jami'i mai kula da kayayyakin yaki na Kamaru Kanal Jean Jacques Fouda, ya ce motocin za su taimaka kwarai kuma kasar bata taba samun tallafin irinsu ba.

Duk da cewa Kanal Fouda bai fadi adadin motocin ba, rahotanni na cewa guda shida kuma an taba amfani da su a kasar Afghanistan.

A farkon makon nan ne gwamnatin fadar Amurka ta sanar da tura dakaru 90 zuwa Kamaru, wadda ke daya daga cikin kasashen da kungiyar Boko Haram ke kai hare-harenta.