An samu ci gaba wajen rage talauci a Afrika

Shugaban bankin duniya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban bankin duniya

Shugaban bankin duniya Jim Yon Kim zai kaddamar da wani rahoto kan rage talauci a kasashen duniya musamman a kasashen Afrika a ranar lahadi a Accra babban birnin kasar Ghana

A jawabin da yayi dangane da ranar, shugaban babban bankin duniyar ya ce kasashen Africa sun samu ci gaba wajen rage talauci a 'yan shekarun da suka gabata to amma rikice-rikice da kuma yakin basasa na cikin abubuwan da ke taka musu birki.

Ya ce a cikin shekara ta 2012 mutane sama da miliyan 300 ne suke fama da talauci amma adadin ya ragu yanzu .

Mr Kim ya ce wasu kasashen Afrika sun yi kokari wajen bunkasa harkar noma ya yinda wasu sun zuba jari a fanin illimi kuma suna cikin dalilan da suka haifar da wannan sakamako.