Hungary ta rufe iyakarta da Croatia

Hakkin mallakar hoto AP

Kasar Hungry ta rufe kan iyakokinta da kasar Croatia a wani mataki na hana 'yan gudun hijra kwarara zuwa yammacin turai.

Ministan harkokin waje na Hungry, Peter zijato ya ce ya zama dole kasar tasa ta dauki wannan mataki tunda dai shugabannin tarayyar turai sun gaza yin amfani da karfi wajen hana kwararar masu kaura shiga Girka.

Kasar ta ce yanzu kuma za ta karkata akalar masu gudun hijrar zuwa kasar Slovenia.

Tuni dai kasar Slovenia ta bakin ministar cikin gidanta, ta ce za ta yi shirin ko-ta-kwana wajen tunkarar kwararar 'yan hijrar da ake son turo mata.