Gwamnan Delhi ya koka kan fyaɗe

Hakkin mallakar hoto Reuters

Gwamnan Delhi, babban birnin India ya zargi gwamnatin tarayya da kuma 'yan sandan da rashin yin abin azo a gani domin kare yara kanana bayan a yi ta yiwa 'yan mata fyade.

A lamari na baya-bayan nan wasu karti maza biyu sun sace yarinya 'yar shekaru biyu, yayin da gungun wasu karti kuma suka yiwa yarinya 'yar shekaru biyar fyade.

Koda acikin makon jiya masu shirin yin fyade sun aukawa wata yarinya 'yar shekaru hudu hari.

Shekaru biyu da suka gabata ne India ta tsaurar dokokin yaki da cin zarafin mata bayan gungun wasu karti sun yiwa wata daliba fyaden da yayi ajalinta a birnin Delhi.