Guzman ya sake layar zana a Mexico

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption El Chapo Guzman dai ya tsere daga gidan yarin Mexico.

Hukumomi a kasar Mexico sun ce kadan ya rage su damke madugun masu safarar kwaya a kasar,El Chapo Guzman wanda ya tsere daga gidan yari a watan Yulin shekarar 2015.

Sai dai kuma Jami'an tsaron kasar ta Mexico ba su yi karin bayani ba dangane lokaci da kuma wurin da aka yi kokarin kama madugun ba.

Amma sun ce Guzman din ya ji rauni a kafa da fuskarsa a kokarin guje wa ma'aikatan.

Shi dai Guzman ya tsere daga gidan yari ne ta wata hanyar kasa mai tsawon kilomita daya da rabi.

Ya kuma kasance madugun kungiyar safarar miyagun kwayoyi wadda tayi kaurin suna wajen safarar kwayoyin zuwa Amurka.