Syria: Dakaru sun kwace ikon Al Huwayjinah

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana ci gaba da fafatawa tsakanin dakarun Syria da amsu tayar da kayar baya

Rahotanni na cewa, dakarun Syria sun kwace iko da garin Al Huwayjinah mai matukar muhimmanci da ke kusa da gari mafi girma a kasar wato Aleppo.

Dakarun gwamnati dake samun tallafin hare-haren jiragen yaki na Rasha, da kuma wasu kungiyoyin mayaka na sa kai, suna kaddamar da farmaki a kan 'yan tawaye daga kudancin birnin.

An raba iko da Aleppo da garuruwan da ke kewayensa a kusa da iyaka da Turkiyya tsakanin gwamnatin Syria, da kuma masu tayar da kayar baya dake yakar shugaba Bashar Al Assad, da kuma kungiyar IS mai ikirarin jihadi.

Kusan shekaru hudu kenan ana gwabza yaki a Syria wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama dy kuma raba miliyoyin mutane da muhallansu.