Yan gudun hijira 600,000 sun shiga Turai

Hakkin mallakar hoto AFP

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce yawan 'yan gudun hijira da suka shiga Turai cikin wannan shekarar ya kai 600,000 ya zuwa yanzu.

Wannan adadi dai ya ninka yawan 'yan gudun hijirar da suka shiga Turai bara har sau uku.

Alkalumma sun nuna cewa yawancinsu sun shiga Girka daga Turkiyya ta teku.

Wakiliyar BBC ta ce alkalumman hukumar 'yan gudun hijirar na cewa fiye da rabin 'yan gudun hijirar sun fito ne daga kasashen da ke fama da tashin hankali kamar su Syria da Afghanistan da kuma Iraki.

Wani kason na 'yan gudun hijirar sun tsallaka Turai ne ta tekun Bahr Rum daga Libya zuwa Italiya.

Karin bayani