Masar: Ana zaben 'yan majalisa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu masu kada kuri'a na ganin samun majalisar dokoki zai sa a samu masu sa ido kan al'amuran gwamnati

Jama'a a kasar Masar suna jefa kuri'a a zaben 'yan majalisar dokoki da aka sha jinkirtawa.

Karon farko kenan da ake yin irin wannan zabe tun bayan da tsohon babban hafsan sojan kasar Abdulfattah Al Sisi ya kwace mulkin kasar shekaru biyu da suka gabata.

Wata mai kada kuri'a Riham Handous tace, kamata yayi jama'a su fito su jefa kuri'a saboda a samu majalisar dokoki da zata sa ido a kan gwamnati."

An dai haramtawa kungiyar Muslim Brotherhood shiga zaben. Kuma jiga-jigai a gwamnatin Hosni Mubarak suna takara a zaben.