Slovenia za ta bar iyakarta a bude

Wasu 'yan gudun hijira da suka iso Slovenia Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu 'yan gudun hijira da suka iso Slovenia

Daruruwan masu gudun hijra suna ta faman ketara wa zuwa cikin kasar Slovenia daga Croation, tun bayan da kasar Hungary ta rufe kan iyakokinta.

Gwamnatin ta Slovenia ta tabbatar wa da masu hijrar cewa za ta kyale su su ratsa ta kasar domin nausawa zuwa kasar Austria, madamar kan iyakokinta suna bude.

Yanzu haka an kakkafa sansanoni ga 'yan hijra a kasar, duk kuwa da cewa Sloveniar ta ce za ta karbi mutane dubu biyu da dai biyar ne kawai.

Hukumar kula da yan gudun hijira ta Majalisar dinkin duniya ta ce da dama daga cikin 'yan gudun hijirar da suka tsalaka cikin Slovenia 'yan kasashen Syria da Afghanistan da kuma Iraki ne.