Mutane 13m basu da ilimin kwamfuta a Burtaniya

Hakkin mallakar hoto
Image caption Masu amfani da na'urorin kwamfuta

Wata gidauniya mai fafutukar bunkasa ilimin sarrafa na'urorin zamani ta yi gargadin cewa fiye da mutane miliyan 12 da wasu miliyan daya masu kananan sana'o'i a Burtaniya ba su da ilimin amfani da kwamfuta don bunkasa harkokinsu.

Gidauniyar mai suna Go.On UK ta fitar da wata taswira dake nuna yankuna a Burtaniya da za a bar mutane a baya ta fannin sarrafa na'urorin da suka danganci kwamfuta.

Gidauniyar ta ce a Wales, fiye da kashi uku cikin hudu na jama'ar birnin basu da ilimin amfani da kwamfuta ta hanyoyi biyar.

Hanyoyi biyar din da ke nuna mutun yana da ilimin sarrafa kwamfuta suna; amfani da kwamfuta wajen tattala bayanai, da sadarwa da wasu, da yin sayayya ta kwamfuta, da magance matsaloli da ita da kuma kuma yin wasu abubuwa ta intanet.

Sai dai London da Scotland da gabashin Anglia sun kasance a gaba-gaba inda fiye da kashi 80% na mutanensu ke da ilimin sarrafa na'urorin na zamani.

Sakamakon binciken da gidauniyar ta gudanar ya nuna cewa maza sun fi mata ilimin sarrafa na'urorin a Burtaniya inda suke da kashi 80% yayin da mata ke da kashi 74%.

Gidauniyar ta tattara bayananta ne ta hanyar wani bincike a kan mutane dubu 4 a fadin Burtaniya inda a ka gwada iliminsu, da bayanai game da zurfin karatunsu, da kudin shigarsu da lafiyarsu da kuma yadda suke iya samun intanet.