Cin Hanci: EFCC ta gayyaci Dakingari

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dakingari ya fadi zabe a kokarin zuwa majalisar dattawa

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Nigeria, EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan jihar Kebbi, Saidu Usman Dakingari domin ya masa tambayoyi a kan zargin wawure dukiyar al'umma.

Kakakin EFCC, Mr Wilson Uwujaren ya tabbatar wa BBC cewar da safiyar ranar Litinin aka gayyaci Dakingari inda ya je ofishin na EFCC a Abuja domin ya amsa tambayoyi.

Dakingari wanda ya shafe shekaru takwas a matsayin gwamnan jihar Kebbi daga shekarar 2007 zuwa 2015 a karkashin inuwar jam'iyyar PDP kuma ya na daga cikin manyan 'yan siyasa da ake zargin da cin hanci a Nigeria.

Ko a ranar Juma'a ma sai da EFCC din ta damke, tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom Mr Godswill Akpabio wanda a yanzu shi ne shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawan kasar, shi ma a kan zargin cin hanci da karbar rashawa.

A yanzu haka dai EFCC na binciken wasu daga cikin tsofaffin gwamnoni a Nigeria ciki har da Alhaji Sule Lamido na Jigawa da Murtala Nyako na Adamawa da Gabriel Suswan na Benue da kuma Ikedi Ohakim na jihar Imo.