Masar: An bayar da hutu saboda zabe

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutane ba su fito zaben sosai ba

Hukumomi a kasar Masar sun bai wa ma'aikatan gwamnati hutun rabin rana a ranar Litinin, a wani yunkuri na ganin an kara samun mutanen da za su fita domin yin zabe a rana ta biyu, ta zaben 'yan majalisun dokoki.

Jami'ai sun yi kiyasin cewa rashin fitowar mutane zuwa rumfunan zabe ya kai kashi biyu cikin dari, kuma kusan dukkanin wadanda suka fito rumfunan zaben ma dattawa ne.

Ana tsammanin magoya bayan Shugaba Al-Sisi ne za su mamaye sabuwar majalisar dokokin.

Masu aiko da rahotanni sun ce wani maudu'in da ke jan hankali a shafin Twitter shi ne 'babu wanda ya je zabe'.