An soma shari'ar likita 'yar Nigeria a Ingila

Image caption Matan uku sun musanta yin sakaci a aikinsu

Wata likita a Ingila ta bayyana gaban kuliya bisa zargin aikata kisan wani yaro dan shekaru 6 ba da niyya ba.

Ana zargin Dr Hadiza Bawa-Garba da yin sakaci kuma abin da ya janyo rasuwar yaron kenan.

Dr Hadiza Bawa-Garba ta shaida wa masu taimaka wa alkalai yanke hukunci cewa tun tana karama a Nigeria ta ke son yin aikin likita.

An shaida wa kotun cewar iyayenta ne suka turo ta nan Ingila karatu kuma ta samu shaidar zama likita a makarantar koyan aikin likita ta Leicester Warwick.

Ana zargin Dr Hadiza Bawa-Garba da wasu ma'aikatan jiyya su biyu, Theresa Taylor da Isabel Amaro da aikata kisa bada niyya ba a asibitin Leicester Royal infirmary a watan Fabarairun 2011.

Dukkansu ukun sun musanta laifin yin sakaci da aiki kuma ana ci gaba da sauraron shari'ar.