Korafe-korafe kan wasu ministocin Buhari

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Buhari na shirin sanar da ma'aikatun da ministocin za su jagoranta

Ana ci gaba da samun korafe-korafe a kan wasu daga cikin sunayen da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar wa majalisar dattawa domin nada su a matsayin ministoci.

Na baya-bayan nan shi ne korafin da jam'iyyar APC reshen jihar Sokoto ta gabatar idan take adawa da bai wa Hajiya Aisha Abubakar mukamin minista daga jihar.

A cikin wata takardar koke da jam'iyyar ta rubuta wa shugaban kasar bayan wani taron da gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal ya jagoranta, reshen jam'iyyar ya ce Hajiya Aishatu Abubakar ba ta da katin zama mamba ta kowace jam'iyya, abin da ya sabawa sashe na 62 sakin layin na biyu na kundin tsarin mulkin kasar.

Sai dai wannan na zuwa ne a daidai lokacin wasu masu goyon bayan ta ke ci gaba da zanga-zangar lumana da kuma taruka da 'yan jarida domin nuna rashin amincewarsu ga nema sauya sunanta.

'Shiyyoyin Siyasa'

Can kuma a jihar Yobe, wasu kungiyoyi sun gabatar da korafi a kan mika sunan Hajiya Khadija Bukar Abba Ibrahim a matsayin minista inda suka ce hakan ya sabawa tsarin rarraba mukamai a tsakanin shiyyoyin siyasar jihar.

A cewar su, da Hajiya Khadija da kuma gwamnan jihar, Ibrahim Gaidam duk 'yan shiyyar siyasa ta Yobe ta gabas ne, kuma mijinta, watau Sanata Bukar Abba Ibrahim shi ne sanata da ke wakiltar shiyyar.

Dama dai ana gabatar da korafe-korafe a kan mika sunan tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi da kuma mutumin da aka gabatar da sunansa daga jihar Oyo, watau Barrister Adebayo Shittu.

A ranar Talata ne ake sa ran majalisar za ta koma zaman ci gaba da tantance mutanen da shugaba Buhari ke son nada wa a matsayin ministoci.

A ranar Alhamis da ta wuce ne, majalisar dattawan ta amince da sunayen mutane 18 domin a nada su a matsayin ministoci.