Ramon Vega zai tsaya takarar shugaban Fifa

Tsohon dan wasan Tottenham, Ramon Vega, yana tunanin tsayawa takarar shugabancin hukumar kwallon kafar duniya, Fifa.

Fifa ta dakatar da shugabanta, Sepp Blatter da mataimakinsa Michel Platini daga aiki na tsawon kwanaki 90 bisa zargin karbar hanci.

'Yan kwamitin koli na hukumar za su yi taro ranar Talata domin tattaunawa a kan ko za su dage zaben da za a yi a watan Feburairu.

Tsohon dan wasan Switzerland, wanda ya bugawa Celtic da kuma Watford, ya yi aiki a ma'aikatun kula da kudi daban-daban tun da ya yi ritaya a shekarar 2004.