Dubban 'yan cirani sun makale a Slovenia

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'yan cirani

Dubban 'yan cirani sun makale a iyakokin kasashen Slovenia da kuma Croatia a yayin da aka sanya sabon takunkumi na dakatar da shigarsu tarayyar Turai.

Mutane da dama -- wadanda suka hada da iyalai da kananan yaran da ba su da muhalli -- na kwana a cikin sanyi da kuma ruwa a garin da ba na kowa ba a tsakanin Slovenia da kuma Croatia.

Jinkirin ya kara yawan mutane a kan hanyar Balkan tunda Slovenia ta sanar a ranar Lahadi cewar ba za ta iya karbar 'yan ciranin da ba su da adadi ba.

Motoci kirar bas cunkushe da mutane sun nufi kudancin Serbia.