Boko Haram: Kamaru za ta sayo jiragen yaƙi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A makon jiya ne Amurka ta aika da sojinta 300 zuwa Kamaru domin murkuseh Boko Haram.

Gwamnatin Kamaru ta bai wa wani kamfanin Amurka kwangilar samar mata jirage marasa matuka guda shida wadanda za su taimaka wa dakarun kasar yaki da 'yan kungiyar Boko Haram.

Ana kiyasta cewa za a kashe CFA 5,000,000,000 wurin sayen jiragen, wadanda za su rika kai hare-hare a arewacin kasar, inda 'yan Boko Haram suke ayyukan ta'addanci.

A makon jiye ne dai Amurka ta aika da sojoji 300 zuwa kasar Kamaru domin su taimaka wa dakarunta wajen tattara bayanai da sa ido da kuma shawagi a maboyar 'yan ta'adda.

Kazalika, Amurka ta bai wa kasar agajin motoci masu sulke.