Assad ya kai ziyarar ba-zata Moscow

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugabannin biyu sun tattauna kan hare-haren da Rasha ke kai wa a Syria.

Shugaban Syria Bashar al-Assad ya kai ziyarar ba-zata kasar Rasha inda ya gana da Shugaba Vladimir Putin a birnin Moscow.

Shugaba Assad a lokacin wannan ziyarar, ya gode wa Mr Putin saboda taimakon da yake samu inda ya ce ba domin Rasha ba, to da ta'addanci ya yadu fiye da wuraren da ake yanzu lamarin ya yi kamari.

Ana shi bangaren shugaba Vladmir Putin ya ce luguden wuta da kasarsa ke yi a Syria zai taimaka wajen samun maslaha a siyasance.

Mr Putin yace "Syria kasa ce da muke kawance kuma a shirye muke mu ba ta gudunmuwa ba wai ta hanyar yaki da ta'addanci ba kadai amma kuma har ta tsarin siyasa da kuma hada kai da wasu kasashe masu karfin fada a ji a wannan shiyyar, musamman wadanda ke son a samu zaman lafiya."

A karshen watan jiya ne Rasha ta kaddamar da hare-hare ta sama a Syria.

Gwamnatin Rashan ta ce tana kai hare-haren ne a kan 'yan kungiyar IS da ke ikirarin kishin Musulinci da kuma sauran masu tayar da kayar baya da ke yaki da gwamnatin Mr Assad.

Wannan ziyarar dai sako ne da Shugaba Putin yake aikewa kasashen yammacin duniya a kan cewar da Rasha na da rawar da za ta taka a gabas ta tsakiya kuma babu yadda za a shawo kan rikicin Syria ba tare da an saka Rasha a ciki ba.