Harbe-harbe a Congo Brazzaville

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Al'ummar Congo na tsaka mai wuya

An ji karar harbe-harbe a Brazzaville babban birnin Congo, inda magoya bayan 'yan adawa suke kokarin yin maci zuwa birnin.

Hukumomin kasar sun haramta duk wata zanga-zanga tun kafin a gudanar da wani zaben raba gardama mai cike da rudani a karshen makon nan kan batun ko za a kyale shugaba Denis Sassou Nguesso ya tsaya takara a karo na uku.

Wakiliyar BBC ta ce "Masu adawa sun bayyana wannan kuri'ar raba gardama tamkar yi wa kundin tsarin mulki hawan kawara ne."

Wani mai aiko da rahotanni ya ce an yi wa birnin kawanya, kuma babu cunkoson motoci a kan tituna.

Shugaba Denis Sassou Nguesso mai shekaru 71 yanason ya ci gaba da mulki bayan da ya shafe shekaru 32 yana mulkin kasar.