An dage shari'ar da ake yi wa Saraki

Image caption Saraki ya musanta zarge-zargen da ake yi masa.

Kotun kula da da'ar ma'aikata ta Najeriya, ta dage shari'ar da take yi wa shugaban Majalisar dattawan kasar Bukola Saraki kan zargin yin karya wajen bayyana kadarorinsa.

Kotun ta ce ta dage shari'ar ne saboda Saraki ya kai kara zuwa Kotun daukaka kara inda yake son sanin ko kotun da'ar ma'aikatan tana da hurumin sauraren kara a kansa.

Sai dai kotun ta amince da bukatar lauyoyin masu shigar da kara cewa a koma gaban ta ranar biyar da shida ga watan Nuwamba domin ci gaba da sauraren karar, ganin cewa kafin lokacin kotun daukaka karar ta yanke hukunci kan bukatar Saraki.

Saraki ya gurfana a gaban kotun ne bisa zarge-zarge goma sha uku -- cikin su har da zargin yin karya wajen bayyana kadarorin da ya mallaka.

Ya musanta zarge-zargen a lokacin da ya fara gurfana a gaban kotun ranar 22 ga watan Satumba.

'Yan Majalisa sun yi masa rakiya

Saraki ya isa kotun da ke Abuja ne tare da rakiyar 'yan majalisar dattawan kasar su fiye da tamanin.

A cikin 'yan majalisar dattawan har da: mataimakin shugaban majalisar, Sanata Ike Ekweremadu da shugaban masu rinjaye, Sanata Ali Ndume da Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da Sanata Dino Melaye da Sanata Danjuma Goje.