Jam'iyyar adawa a Canada ta lashe zabe

Image caption Magoya bayan jam'iyyar Liberal Party a Canada

Jam'iyyar adawa ta Liberal Party a Canada wadda Justin Trudeau ke jagoranta ta samu gagarumar nasara a babban zaben kasar da aka gudanar.

Jam'iyyar ta Liberal Party ta lashe dukkan kujeru a dukkan larduna 4 dake yankin da ke da ruwa, kuma hakan ya sa ta samu isassun kujeru a majalisar dokokin kasar da za ta kafa gwamnati.

Kimanin shekaru 10 kasar ta kasance karkashin jagorancin gwamnatin da ake gani ta masu ra'ayin mazan jiya ne ta Firayiminista Stephen Haper.

Mista Harper ya amince ta kayen da yasha, lokacin da ya kira Mista Justin Trudeau cikin dare.

Mr Justin Trudeau dan shekara 43 kuma dandan tsohon Firayiministan kasar Pierre Trudeau, ya yi wa jama'ar kasar alkawarin kawo sauye sauya a lokacin da suke yakin neman zabe.

A wajen mutanen Canada da dama, a bangare guda, wannan zabe tamkar zaben raba gaddama ne ga tsatsauran tsarin tafiyar da mulki na Firayiminista Harper, sannan dayan bangaren zaben wanda suke gani shi zai sake dawo da tattalin arzikin kasar kan turba.