Shugaban China ya soma ziyara a London

Image caption Shugaba Xi tare da Sarauniya Elizabeth

Shugaba Xi Jinping na China ya isa fadar Buckinghm a ranar farko ta ziyarar da ya kai Biritaniya.

Daruruwan mutane 'yan china mazauna Biritaniya sun taru a tsakiyar birnin London domin su ga wucewar Mista Xi cikin keken dawaki na sarauniyar Ingila.

An kuma gudanar da wasu kananan zanga-zanga don nuna adawa kan keta hakkin bil'adama da ake yi a China, amma wasu masu adawa da zanga-zangar sun hana wasunsu wucewa.

Zuwa jimawa ne mista Xi zai gabatar da jawabi a gaban majalisun dokokin kasar biyu kafin ya halarci liyafa a fadar sarauniya Elizabeth.

A lokacin ziyarar, ana sa ran gwamnatin Biritaniya za ta kulla yarjejeniyar kasuwanci da China ta kusan dala biliyan 50.