Jonathan ya shawarci 'yan takara a Tanzania

Image caption Jaridun Tanzania sun yi tsokaci sosai kan shawarar da Jonathan ya bai wa 'yan takarar.

Shawarar da tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya bai wa 'yan takarar shugabancin kasa a Tanzania ita ce ta fi daukar hankulan jaridun kasar.

Mr Jonathan -- wanda ke kasar ta Tanzania a matsayin shugaban tawagar kasashen kungiyar Commonwealth da za ta sa-ido -- ya bukaci 'yan takarar da ka da su zubar da jini a zaben da za a yi a ranar Lahadi mai zuwa.

Mr Jonathan dai ya amince da shan kaye a zaben da aka yi a Najeriya a watannin Maris da Aprilu, wanda dan takara a karkashin jam'iyyar hamayya ta APC, Muhammadu Buhari ya yi nasara.

Shugaban babbar jam'iyyar hamayya, wato Chadema a kasar ta Tanzania, Freeman Mbowe , ya ce suna da kwarin gwiwar kayar da jam'iyyar Chama Cha Mapinduzi (CCM) , wadda ke mulkin kasar tun da ta samu 'yancin kai a shekarar 1964.