Kwayoyin cutar Maleriya na yaɗuwa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Cutar Maleriya ta hallaka miliyoyin yara a Afrika

Wani binciken kimiyya da aka gudanar ya nuna damuwa kan yadda kwayoyin cutar maleriya ke yaduwa a kudu maso gabashin Asiya da cewa za su iya bazuwa zuwa Afrika.

Hakan zai sanya rayuwar mutane da dama cikin hadari.

Wasu gwaje-gwajen kimiyya da aka gudanar sun nuna yadda kwayoyin cutar zazzabin cizon sauro wadanda ke bijirewa maganin artimisinin mai matukar tasiri, suka yada nau'uka na zazzabin cizon sauro.

Hukumar lafiya ta Amurka wadda ta gudanar da binciken, ta yi gargadi cewa yaduwar cutar za ta iya jawo gagarumar matsala.

An wallafa sakamakon binciken ne a mujallar 'Journal Nature'.

Hukumar lafiya ta duniya ta kiyasta cewa yawan mutuwar da ake samu a duniya daga cutar maleriya ta ragu da kashi 60 cikin shekaru 15 da suka gabata.