'Jiragen Rasha sun kashe mutane 45 a Syria'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jiragen yakin Rasha sun kai hari Syria

Wata kungiyar masu sanya idanu a Syria ta ce a kalla mutane 45 sun rasa rayukansu sakamon hari ta saman da jiragen saman Rasha suka kai wa 'yan tawayen da ke zaune a yankin arewa maso yammacin Syria.

Kungiyar, mai suna Syrian Observatory for Human Rights , ta ce jiragen yakin Rasha sun jefa bama-bamai a yankin Jabal al- Akrad wanda ke a lardin Latakia da yammacin ranar Litinin.

Kwamandan kungiyar 'yan tawayen Free Syrian Army wadda ke samun goyon bayan kasashen yamma da kuma iyalan 'yan tawayen na daga cikin wadanda suka rasa rayukan nasu.

Rasha dai ta ce ta kai wa masu tayar da kayar baya na kungiyar IS hari a ranar Litinin.

Sai dai kuma masu fafutuka sun ce 'yan kungiyar masu jihadin ba su da yawa a wannan yankin da aka kai wa harin.

A shekarar 2012 ne kungiyar masu jihadin ta kwace ikon yankin na Jabal al-Akrad.