Amurka da Rasha sun cimma yarjejeniya

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Mista Putin da shugaba Obama

Amurka da Rasha sun rattaba hannu a wata yarjejeniyar fahimtar juna domin rage yiwuwar jiragen yakin kasashen biyu a sararin samaniyar Syria su yi arangama da juna.

Hakan ya zo ne bayan Amurkan ta zargi Rasha da gangancin lulawa da jiragen yakin ta kusa-kusa da na dakarun kawance dake yaki da kungiyar IS A Syria.

Ba a dai bayyana abubuwan da yarjejeniyar ta kunsa ba, amma ma'aikatar tsaro ta Pentagon ta ce Rasha ce ta ne mi a kulla ta.

Wakilin BBC a Washington ya ce yarjejeniya ba ta shafi tsara kai hare hare kan mayakan kungiyar ta IS ba, ko tattara bayanan sirri game da kungiyar ta IS.

A cikin wata sanarwa, ma'aikatar tsaro ta Pentagon ta ce sharuddan yarjejeniyar sun kunshi bangarorin biyu su bi ka'idodjin lulawa da jirage a sararin samaniyar Syria, da rashin yiwa juna shisshigi a hanyoyin sadarda bayanai da jirage ke amfani da su.