Ba zan tsaya takara ba - Biden

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mr Biden ya rufe bakin masu yada jita-jita

Mataimakin shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya kawo karshen jita-jitar da ake ta yadawa ta batun takararsa, inda ya ce ba shi da niyyar tsayawa takarar shugaban kasar a zaben da za a yi shekara mai zuwa.

Da yake magana tare da Shugaba Obama da kuma mai dakinsa Jill a fadar White House, Mr Biden ya ce shi da iyalinsa na makokin dansu ne da cutar Kansa ta kashe, kuma ya tabbatar ba shi da lokacin yakin neman zaben da zai kai ga nasarar tsayar da shi dan takarar jam'iyyarsa ta Demokrat.

Ya ci gaba da cewa duk da cewa ba zai tsaya takarar ba amma dai ba zai yi shiru a lokacin yakin neman zaban ba.

Masu aiko da rahotannin sun ce sanarwar ta sa zata sa babbar 'yar takarar shugaban kasar ta Jam'iyyar Demokrat din, Hillary Clinton, samun sa'ida.