Amurka ta bai wa Nijar jiragen yaki

Hakkin mallakar hoto
Image caption Jirgin sama na yaki

Amurka ta taimaka wa gwamnatin Jamhuriyar Nijar da jiragen yaki biyu da motocin 30 da kuma wasu kayayyaki domin yaki da ta'addanci.

Jiragen na dauke da na'urorin zamani na tattara bayanai, kuma za su taimaka na Nijar wajen gano barazanar 'yan ta'adda da kuma kare iyakokin kasar.

Darajar jiragen da motocin da Amurkan ta bai wa kasar ta kai Yuro miliyan 32.

Jamhuriyar Nijar dai na fama da matsalar masu tayar da kayar baya na Boko Haram, inda ko a ranar Laraba suka kashe sojojin kasar guda biyu.