Buhari ya nada sabon shugaban INEC

Image caption Mutane su fito da dama a zaben 2015

Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya nada Farfesa Mahmood Yakubu a matsayin sabon shugaban hukumar zaben kasar, INEC.

Nadin ya biyo bayan taron majalisar kasa da shugaban ya jagoranta ne a fadarsa da ke Abuja.

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal shi ne ya sanar da manema labarai abubuwan da taron na majalisar koli ya cimma.

Sannan kuma taron ya amince da nadin wasu kwamishinonin zabe;

  • Mrs. Amina Zakari (Arewa maso yamma)
  • Dr. Anthonia Okoosi-Simbine (Arewa ta tsakiya)
  • Alhaji Baba Shettima Arfo (Arewa maso gabas)
  • Dr. Mohammed Mustafa Lecky (Kudu maso kudu)
  • Mr. Soyebi Adedeji Solomon (Kudu maso yamma)

Taron ya amince Ambasada Lawrence Nwuruku ya ci gaba da wakiltar shiyyar Kudu maso gabashin kasar a hukumar ta INEC.