An ci tarar shagon sayar da magani ta intanet

Image caption Kwayoyin magani

An ci tarar wani shagon sayar da magani ta intanet Pharmacy2U Fam 130,000 saboda ya sayar da bayanan masu hulda da shi ga wasu kamfanonin saye da sayar wa.

An sayar da bayanan mutanen ga kamfanoni da dama, ciki har da wani da a ka taba jan kunnensa saboda tallar yaudara da ya yi, da kuma wani kamfanin da ake gudanar da bincike a kan sa saboda wata cacar tikiti da ya shirya.

Ofishin kwamishin labarai a Burtaniya ya ce shagon Pharmacu2U ya yi kuskure sosai wajen sayar da bayanan masu mu'amala da shi dubu 20.

Shagon Pharmacy2U, wanda shi ne mafi girma da aka amince ya rika sayar da magani ta intanet a Burtaniya ya sayar da bayanan kowadanne mutane dubu daya a kan Fam130, kuma mutanen sun hada da masu fama da Asma da rashin karfin mazakuta da kuma wasu cututtuka da ke kama wadanda suka cimma wasu shekaru ko kuma wani jinsi na daban.

Wani mataimakin kwamishina a ofishin yada labaran, David Smith ya ce shagon Pharmacy2U ya saba ka'idojin kare bayanan batare da ya nemi izinin masu bayanan ba.