Daliban Afrika ta Kudu suna zanga-zanga

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A cewar daliban matakin gwamnatin bai dace ba

Dalibai a Afirka ta Kudu sun yi kiran da a rufe baki dayan jami'o'in kasar a matsayin nuna kin amincewa da karin kudin makarantar da aka yi.

Dalibai da dama ne aka raunata a lokacin da 'yan sanda suka harba hayaki mai sa kwalla da harsasan roba a kan masu zanga-zanga a Jami'ar Nelson Mandela a Port Elizabeth.

A ranar talata ne dabilan suka ka yi watsi da wani tayin da gwamnati ta yi na karin kashi shida cikin dari na kudin makarantar a shekara mai zuwa.

Masu zanga-zangar sun ce karin kudin makarantar zai hana 'ya'yan talakawa bakar fata zuwa jami'a.