Maharba sun hallaka 'yan Boko Haram

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Maharba a Maiduguri

Dakarun sojin Nigeria tare da hadin gwiwar wasu maharba sun yi arangama da 'yan Boko Haram inda suka hallaka da dama daga cikin mayakan kungiyar.

Dan majalisa wakilai mai wakiltar mazabar Michika da Madagali a jihar Adamawa, Honorabul Adamu Kumale shi ne ya tabbatar wa da BBC, amma kuma bai bayyana adadin 'yan Boko Haram din da aka kashe ba.

Sai dai rahotanni sun ambato wasu daga cikin maharban na cewar sun kashe 'yan Boko Haram kusan 150 a yankunan Madagali da kuma Gwoza.

Bayanai sun ce a lokacin tashin hankalin da aka yi a daren Talata, sojojin tare da maharban sun kubutar da mata da kananan yara kusan 36 daga hannun 'yan Boko Haram.

Rikicin Boko Haram da aka shafe shekaru shida ana fafatawa, ya janyo rasuwar mutane kusan 20,000.

Mayakan Boko Haram na tafka ta'asa a kasashen Nigeria da Nijar da Kamaru da kuma Chadi inda gwamnatocin kasashen suka kafa runduna guda domin murkushe 'yan kungiyar.