Kerry ya shawarci Isra'ila da Falasdinu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Zaman dar-dar na karuwa a birnin kudus

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, ya yi kira ga Isra'ila da Falasdinawa su kauce wa duk wani abin da ka iya rura wutar rikici a wani yunkuri na kawo karshen tashin hankali a tsakaninsu.

Mista Kerry ya bayyana hakan ne a Berlin, inda yake ganawa da Firai ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu.

Mista Netanyahu ya ce Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas, da kungiyar Hamas, da wasunsu ne suka ingiza hare-haren da Falasdinawa suka rika kaiwa da wuka a kan Isra'ilawa a 'yan kwanakin nan.

A tashe-tashen hankula na baya-bayan nan, dan Isra'ila ya ji mummunan rauni bayan da wasu Falasdinawa suka caccaka masa wuka yayin da yake tsaye a wata tashar motar safa a wajen birnin Kudus.

'Yan sanda sun bude wuta a kan maharan, sun kuma kashe daya daga cikinsu, sannan sun raunata daya.

A wani lamarin na daban kuma, sojoji sun bindige wani dalibi Bayahude bayan sun yi zaton cewa wani Bafalasdine ne zai kai hari.