Motar Tesla mai tuka kanta tana da hadari

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yadda ake tunanin motocin za su kasance a nan gaba

Wasu hotuna da aka dora a kan shafukan intanet sun nuna irin hadarin da ke tattareda motoci masu tuka kansu na kamfanin Tesla.

Hotunan sun bayyana irin tukin ganganci da ake yi da motocin da kuma gudun fanfalaki.

Daya daga cikin hotunan ya bayyana yadda kwatsam motar ta kauce daga kan titi bayan ta saki hannunta daga kan titi birnin Portland na Amurka.

Wani hoton ma ya nuna yadda motar kirar Tesla samfirin Model S ta kwace daga hannun da take sannan kuma ta durfafi wata motar don yin taho mu gama.

Ita dai motar kirar Tesla tana tuka kanta har ma da sauya hannun tuki.

Sai dai kuma a lokacin da ake kaddamar da motar, shugaban kamfanin na Tesla, Elon Musk ya ce daman motar an fito da ita ne domin gwaji.

Ya ce " manhajar da aka sanyawa motar sabuwa ce."

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Motocin na Tesla dai za su iya shiga cikin turmutsun motoci kuma su fita

Sai dai kuma ya kara da cewa " muna takatsantsan a wannan lokacin saboda haka muna jan hakalin direbobi da su kasance a koyaushe hannunsu yana kan sitayari saboda abin da ka iya zuwa ya zo".