Dakarun Amurka sun ceto mutane a Iraki

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun sun je ne saboda ceto mutanen

Rundunar sojin Amurka ta ce sojojinta na kundumbala da takwarorin aikinsu na Kurdawa sun kubutar da mutane da dama da ake garkuwa da su yayin wani hari da suka kai a kan wani gidan yari na kungiyar IS a arewacin Iraki.

Kusan mutane saba'in aka kubutar, sannan aka kashe mayakan kungiyar ta IS mai da'awar kafa kasar Musulunci, aka kuma kama wasu.

Sojan Amurka daya ya mutu a harin.

Wakilin BBC ya ce a cewar ma'aikatar tsaro ta Amurka, Pentagon da gwamnatin Lardin Kurdistan ce ta bukaci a kai harin saboda bayanan sirri na nuna cewa akwai yiwuwar yi wa mutanen kisan gilla.

Mutuwar Ba'ameriken ce ta farko da aka samu a tsakanin dakarun Amurka tun bayan da kasar ta kaddamar da yaki a kan kungiyar IS bara.