'Buhari ba zai iya yakar cin hanci ba'

Hakkin mallakar hoto Buhari Twitter
Image caption Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari

Wani fitaccen dan siyasa kuma tsohon Jakadan Nijeriya a kasar Switzerland, Ambasada Yahaya Kwande, ya ce duk da cewa shugaba Muhammadu Buhari yana da kyakkyawar niyya wajen kawo karshen matsalar rashawa da cin hancin a kasar amma ba zai iya magance wannan matsala ba.

Sai dai kuma ya ce yana sane da irin kokarin da Buharin yake yi da kuma irin tsoron sa da mutane suke yi wadanda ya ce sun taimaka gaya wajen rage matsalar.

Ambassada Kwande ya kara da cewa matsalar rashawa da cin hanci a Najeriya ta yi katutun wadda kawar da ita farad daya zai yi wuya, a inda yake ganin shugaba Buhari zai iya dasa dan-ba ne kawai wanda daga bisani za a mori ribar hakan a nan gaba.

Dangane kuma da zarge-zargen da 'yan jam'iyyar adawa ta PDP suke yi kan cewa yaki da cin hanci da rashawar da gwamnatin Buharin take yi wani abu ne mai kama da bita da kulli, ambassada Kwanden ya ce shure-shure ne kawai wanda aka ce ba ya hana kaza mutuwa.