Rasha ta kara kaimi a kan Syria

Vladimir Putin Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Vladimir Putin

Rasha ta kara kaimi a kokarin da ta ke yi wajen amfani da hanyoyin diplomasiya domin shawo kan rikicin Syria ya yinda ta ke cigaba da kai hare haren bama bamai domin marawa shugaba Bashar al Assad baya.

A ranar Juma'a ministan harkokin waje na kasar Rasha tare da takwarorinsa na kasashen Amurka da Saudiyya da kuma Turkiya za su gana a Veina.

Kasashen uku na goyon bayan 'yan tawaye da ke adawa da gwamnatin Syria kuma sun soki matakin amfani da karfin soja na kasar Rasha a kan Syria..

A jiya Alhamis shugaba Putin ya nanata cewa akwai bukatar ganin cewa kasashen duniya sun hada kai wajen tunkarar mayakan IS .

Ya kuma kara da cewa hare hare ta sama da Rasha ke kai wa za su taimaka wajen ganin an cimma a sulhu a rikicin kasar ta Syria