Za a bai wa ma'aikatan Twitter hannun jari

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jack Dorsey ya sha alwashin kawo sauyi a kamfanin.

Daya daga cikin mutanen da suka mallaki shafin Twitter, Jack Dorsey, ya ce zai bai wa ma'aikatansa kashi uku cikin dari na hannun jarin da ya sanya a kamfanin .

A halin yanzu dai hannun jarin kamfanin ya kai $197m.

Mr Dorsey ya ce zai dauki matakin ne domin "bai wa mutane damar samun walwala."

Shafin na Twitter bai yi karin haske a kan batun ba.

A makon jiya ne kamfanin ya ce zai kori ma'aikata 336 daga aiki.

Daya daga cikin ma'aikatan ya shaida wa BBC cewa sun ji dadi da wannan mataki, yana mai cewa a shirye suke su bai wa Mr Dorsey goyon baya.