Mutane 30 sun mutu a harin Yola

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan kungiyar Boko Haram sun sha kai hare-hare a birnin na Yola.

Hukumomi a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya sun ce mutane 30 ne suka mutu a harin bam din da aka kai a birnin Yola.

Kakakin gwamnatin jihar, Ahmed Sajo, ya shaida wa BBC cewa mutane 96 ne suka samu raunuka.

Wadansu da suka shaida lamarin sun ce an tayar da bam din ne a Masallacin Jambutu da ke Jimeta a dai-dai lokacin da ake tayar da Sallar Juma'a.

Sajo ya ce 'yan kunar bakin wake ne suka tashi bama-baman bayan an tayar da Sallah.