Za a samar da matakai don rage rikicin Kudus

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya ce an cimma matsaya kan rikicin Kudus

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya ce Isra'ila da Jordan sun amince wajen samar da matakai don rage tashe-tashen hankula da ake fama da su a harabar masallacin Al-Aqsa da ke birnin Kudus.

Mista Kerry ya yi wannan magana ne a Jordan wadda ita ce kasar da ke da alhakin kuka da masallacin na Al-Aqsa.

Ya ce matakan da aka amince da su sun hada da sabunta bukatar Isra'ila na tabbatar da dokokin da dama can ake amfani da su a wajen ibadar, da kuma shirin tattaunawa a kan yadda za a karfafa matakan tsaro a wajen.

A baya-bayan nan ne ake ta samun rikice-rikice tsakanin Palasdinawa da Isra'ilawa a yankin masallacin.