An kama mataimakin shugaban Maldives

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mataimakin shugaban Maldives Ahmed Adheeb

An kama mataimakin shugaban kasar Maldives, Ahmed Adheeb dangane da wani yunkuri na kashe shugaban kasar Abdalla Yameen.

Shugaban ya tsallake rijiya da baya cikin watan da ya gabata yayin da Bam ya tashi a wani jirgin ruwa da yake ciki. Lamarin dai ya haddasa raunata mai dakin shugaban kasar:

Wakilin BBC yace tuni dai aka kama 'yan sanda biyu dangane da harin da aka kai wa shugaban kasar, kuma an kama Ahmed Adheeb ne da safiyar ranar Asabar a filin jiragen sama bayan ya dawo daga wata tafiya da ta danganci aiki.

Cikin 'yan shekarun nan dai kasar ta Maldives ta fada cikin rikicin siyasa bayan an daure tsohon shugaban kasar Muhammed Nasheed bisa laifin da ya danganci ta'addanci.