'Yan Agentina na kaɗa kuri'a

Shugabar Agentina Fernandez de Kirchner da ta yi murabus Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasar Agentina ta fuskanci zanga-zangar kin amincewa da yadda gwamnati ke tafiyar da tattalin arzikin kasar.

Al'ummar kasar Agentina na kaɗa ƙuri'a dan zaɓen sabon shugaban kasa, a daidai lokacin da shugaba Cristina Fernandez de Kirchner ta sauƙa daga mukamin ta.

Ta shafe shekaru 8 ta na mulkin da ya gurgunta tattalin arziƙin ƙasar.

Dukkan 'yan takarar shugabancin kasar sun yi alƙawarin farfado da tattalin arzikin kasar, da ya fada halin ni 'ya su, da kuma rage shirye-shiryen da ke lashe kudaden kasar.

Mai farin jini cikin 'yan takarar shi ne, Daniel Scioli wanda ya kasance ɗan gaban goshin shugaba de Kirchner, kuma tsohon ɗan wasan tseren kwale-kwale wanda ya rasa hannunsa a lokacin wata gasar wasanni.

Sai dai ya na fuskantar babban ƙalubale a takarar da ya ke yi da magajin garin Buenos Aires, wato Mauricio Macri, da kuma tsohon abokin shugabar kasar wato, Sergio Massa.