'Boko Haram na iko da ƙananan hukumomi biyu'

Hakkin mallakar hoto Borno Govt

Gwamnan jihar Borno da ke arewacin Najeriya, Alhaji Kashim Shettima ya ce, yanzu ƙananan hukumomi biyu ne suka rage a hannun 'yan Boko Haram daga cikin ƙananan hukumomi 27 a jihar.

Ƙananan hukumomin da suke hannun 'yan Boko Haram, in ji gwamnan su ne; Abadam da Mobbar, da kuma wani ɓangare na ƙaramar hukumar Marte.

Gwamna Shettima ya kuma ce, wannan alama ce cewa, 'yan kungiyar Boko Haram suna rasa madafa a jihar ta Borno.

'Taron samun mafita'

Kashim Shettima ya bayyana hakan ne gabanin taron da ya yi da malaman addini, da limamai, da masu unguwanni da kuma shugabannin hukumomin tsaro domin duba hanyoyin da za a tunkari sabon salon 'yan Boko Haram na kai hari masallatai musamman a birnin Maiduguri da kewaye.

Hakkin mallakar hoto Borno Govt
Image caption Limamai da lawanai sun halarci taron

Taron wanda ya samu halarcin shugabannin soja, 'yan sanda, da kuma na hukumar SSS ya duba irin rawar da malamai da sarakuna za su taka wajen ganin an kare mutane a masallatai daga fuskantar hare-hare.

Gwamnan ya yi nuni da cewa, a baya 'yan Boko Haram suna rike da iko da kananan hukumomi fiye kusan 20 a jihar ta Borno mai kananan hukumomi 27.

Gwamna Shettima ya ce, sabon yunkurin 'yan Boko Haram na zafafa hare-hare a jihar Borno wani salo ne na kawar da hankali daga irin nasarar da ake samu wajen kawo karshensu.

Shi ma Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai Elkanemi a jawabinsa ya bukaci al'umma su bada hadin kai wajen kawo karshen hare-haren Boko Haram.

To sai dai kuma wasu rahotanni na cewa babban hafsan sojojin Najeriya, Laftanar Janar Yusuf Buratai ya musanta kasancewar ko da gari daya a karkashin Boko Haram.