'Yan cirani 11,500 ne ke shiga Croatia a kullum

'Yan cirani cikin tsananin sanyi a iyakar kasar Slovenia
Image caption 'Yan ciranin dai na cikin mummunan yanayi a iyakokin kasashen da za su sada su da nahiyar Turai.

Kasar Croatia ta ce a kowacce rana 'yan cirani 11,500 ne ke shiga kasar, alamun da ke nuna yawan mutanen da ke kokarin shiga nahiyar turai karuwa yake maimakon raguwa.

Ministan cikin gida Domagoj Dzigulovic yace a yau lahadi, adadin mutanen ad suka shiga kasar ya yi matukar yawa tun bayan da 'yan cirani suka fara kara-kaina cikin Croatia a tsakiyar watan Sarumbar da ya gabata.

'Yan cirani sun fara turuwar shiga Croatia ne tun bayan da kasar Hungary ta kare iyakar kasarta da ta hanyar yin katangar waya tsakanin ta da Serbia.

Inda a yanzu suka koma bi ta kasar Turkiyya, kana su shiga kasar Girka daga nan su bulla ta arewacin Macedonia, sai su fada Serbia ta nan kuma su dauki hanyar da za ta kai su Croatia, su kara nikar gari zuwa Slovenia da kasar Austria.

Inda yawancin su ke kokarin shiga kasar Jamus ko Scandinavia, ya yin da su ma a bangaren 'yan sandan kasar suka ce s u na da alkalumma akalla mutane 250,000 da suka shiga Croatia daga watan Satumba kawo yanzu.