An cimma matsaya kan 'yan gudun hijira

Jean Claude Juncker Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jean Claude Juncker

Shugabannin kasashen tsakiyar Turai da na yankin Balkan sun amince da wani tsarin da zai kawo karshen 'yan gudun hijra da ke kwarara zuwa yankunan.

Tsarin -- mai dauke da muradu goma sha bakwai -- ya hada da samar da abinci da wurin zama ga 'yan gudun hijirar sama da dubu dari da suke kan hanyoyin kasashen na Balkan, a inda kuma fiye da rabinsu suke a kasar Girka.

Kasashen kuma sun kara yin alkawarin hada karfi da karfe wajen rubanya sintiri a kan iyakokinsu.

Shugaban hukumar Tarayyar Turai, Jean-Claude Juncker, ya ce hanya daya da za a shawo kan yaduwar 'yan gudun hijrar barkatai ita ce a tsayar da bazuwar su zuwa kasashe.

Ya kuma ce dole ne kasashen su dakatar da kora masu gudun hijrar zuwa kasashen da ke makwabtaka da su saboda hakan yana ta'azzara kokarin da ake yi na rarraba 'yan gudun hijirar.