Kawunan Fulani sun rabu a Nigeria

Image caption Fulanin dai suna son wanke kansu daga zarge-zargen da ake yi musu.

A Najeriya, wasu Fulani mambobin kungiyar Miyetti-Allah sun fice daga kungiyar domin kafa nasu kungiyoyin bisa zargin rashin iya jagoranci.

Kungiyoyin dai sun ce za su yi kokarin magance matsalolin na Fulani da suka ce kungiyar ta Miyetti-Allah ta kasa shawo kansu.

Al'ummar Fulani dai a Najeriya na ci gaba da fuskantar matsalolin zamantakewa tsakaninsu da wasu al'ummomi da kuma manoma a yankuna daban-daban na kasar.

Wani batu a baya-bayan nan da ya kara tunzura Fulanin shi ne na yin garkuwa da tsohon sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya, Olu Falae, wanda aka ce Fulani ne suka je har gonarsa suka yi sace shi.

Al'amarin dai yaso ya kawo zaman tankiya tsakanin Fulani mazauna kudu maso yammacin kasar da masu masaukinsu, wato Yarabawa.

Yanzu haka dai kungiyoyi daban-daban sun tashi tsaye wajen ganin sun goge kashin kajin da ake shafa musu.