'Ba mu sauya matsaya ba kan auren jinsi daya'

Paparoma Francis Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Paparoma Francis

Paparoma Francis ya kammala rangadi na mako uku domin tattaunawa da bishop bishop na darikar katolika kan hanyoyin da za a bi wajen yi wa tsarin zamantakewar aure kwaskwarima,

Sai dai paparoman ya bayyana cewa akwai rarrabuwar kai a tsakanin mabiya darikar katolika dangane da batun.

Paparoma Francis ya ce mutanen suna fake wa da koyarwar darikar su kuma yanke hukunce hukunce masu tsauri akan iyalan da suke cikin halin kunci.

Yayin tattaunawar dai an cimma matsaya akan wasu batutuwa masu dama da suka hada da cewa ba kowane saki tsakanin ma'aurata ne zai haramta yin kome ba.

Sai dai kuma malaman na katolika sun jadadda aniyar cocin na ci gaba da haramta al'adar auren jinsi guda.