'Malamin Shi'a zai fuskanci hukunci'

Hakkin mallakar hoto AP

Kotun ƙolin Saudiyya ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar da aka yi domin ƙalubalantar hukuncun kisa da a ka yanke wa wani fitaccen malami na mazhabar Shi'a.

Sheik Nimr Al Nimr yayi suna wajen goyon bayan boren nuna adawa da gwamnatin Saudiya mabiya Shi'a 'yan tsiraru suka a lokacin guguwar sauyi da ta kaɗa a ƙasashen larabawa.

Halin da malamin ya samu kansa alama ce ta irin iyakar 'yan cin fadin albarkacin baki a Saudiya, da kuma zaman ɗar-ɗar tsakanin 'yan Shi'a da 'yan Sunni.

A Saudi Arabia akwai 'yan Shi'a 'yan tsiraru musamman a yankin Qatif.

Kuma suna kukan cewar, ana nuna muzguna musu, da tauye musu hakkokinsu.